Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da nada sabbin mambobin hukumar jindadin alhazai ta jihar (Muslim Pilgrim Warfare Board), mai mutum 10.
Cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya aikewa manema labarai na nuni da Alhaji Umaru Abubakar Bappari Kem, a matsayin shugaban hukumar.
- Duk Da Matsalolin Da Ake Ciki, Nijeriya Za Ta Ci Gaba Da Bunƙasa – Minista
- Yaƙin Sudan: Gwamnatin Jigawa Ta Samarwa Dalibanta 194 Guraben Karatu A Jami’o’in Cyprus Da indiya
Sauran mambobin hukumar sun hada da Umar Muhammad Yaro, Ibrahim Danmama Umar, da Dakta Bashir Aliyu.
Sai kuma Gidado Liman, Kabiru Mustapha, Aliyu Ibrahim da kuma Alhaji Suleiman Aliyu Bello, sanarwar ta ce nadin ya fara aiki nan take.