• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Nemi A Kafa Dokar Ta-ɓaci Kan Masu Ƙwacen Waya

bySharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
4 months ago
Waya

Kwacen waya babbar gagarumar bahaguwar matsala ce mai zaman kan ta da ta jima ta na ci wa al’umma tuwo a kwarya tamkar a ƙasar da babu doka. 

Akwai matukar damuwa da ban tsoro yadda masu kwacen waya ke aikata mummunar aika- aikar ta hanyar raunata wadanda suka yi wa kwacen ko kuma yi masu kisan gilla a wasu lokutan ta hanyar caka masu wuka.

  • Tattaunawar Da Shugabannin Sin Da Amurka Suka Yi Ta Wayar Tarho Ta Ba Da Jagoranci Ga Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Biyu
  • Wang Yi Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Isra’ila

Al’umma da dama sun nuna damuwar matukar gwamnati da hukumomin tsaro ba su dauki kwararan matakan dakile sace- sacen waya da ya zama tamkar ruwan dare na, to illar da hakan za ta haifar ba karama ba ce.

A Nijeriya musamman jihohin Arewa al’umma na zama cikin zullumin barayin waya wadanda suka mayar da kwacen waya aiki a kullum lamarin da wasu da dama ke ganin dokar ta baci ko agajin gaggawa ce mafitar kawo karshen gawurtacciyar matsalar.

Nijeriya ta fuskanci satar waya miliyan 25 a 2024 wanda hakan kadai ya nuna girman matsalar wadda aka saci waya 2, 854 a kowace awa daga Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024 wanda hakan babban kalubalen matsalar tsaro ne wadda ke karuwa a yayin da ake kara dogara da fasahar waya.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta bayyana hakan a rahoton ayyukan ta’addanci na watanni 12. Rahoton ya bayyana ayyukan ta’addanci miliyan 51.89 da suka shafi iyalai, satar waya ce mafi yawa a ciki da kaso 13.8 da rahoton satar waya miliyan 25.

Rahoton ya nuna akwai layukan waya da ke aiki a wayoyin hannu miliyan 216.66 a Nijeriya haka ma kaso biyu bisa uku a kimanin shekaru 10 da masu yawan shekaru ne ke amfani da wayoyi.

A yayin da duniya ke kara komawa a duniyar fasaha, wayoyin hannu na yi wa al’umma amfani fiye da sadarwa domin suna amfani a matsayin wajen neman ilimi, kasuwanci, karamin banki da biyan bukatun yau da kullum, kuma hanyar rayuwar al’umma da dama wanda hakan ya sa kwacen waya ya zama abin damuwa.

Nazarin ya nuna, a lokacin NBS ta bayar da rahoton mutane miliyan 17.97 ne suka fada tarkon masu kwacen waya. Daga ciki akwai Dorcas Oluwaseyi wadda aka sace wayar ta a cikin mota. “Sun kwace jaka ta, suka dauki karamar jaka ta, suka dauke waya, da katukan ATM di na.”

A yau bata gari suna farautar wayoyin hannu a al’ummar da kunci da tsadar rayuwa ta yi wa katutu, a yayin da raunanan hukumomin tsaro suka bar ta’addancin na ci gaba da faruwa a kullum.

Hukumomin tsaro a lokuta daban-daban kan bayyana kokarin da suke yi wajen kawar da ta’addancin kwacen waya sai dai al’umma na kukan kokarin jami’an ba wani abin rubutawa ba ne a bisa ga yadda matsalar karuwa take yi maimakon raguwa.

Jihar Kano ce kan gaba a Arewacin Nijeriya inda kwacen waya ya yanke cibi ta yadda barayin ba sani ba sabo suka mayar da ‘ya’ya da yawa marayu, suka mayar da mata zawarawa suka raba dimbin al’umma da mahaifan su, duka a dalilin kwace wayoyin wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

Kisan gillar da wani mai kwacen waya ya yi wa matashin jami’in sojin ruwan Nijeriya a Kaduna a kan ya ki aminta ya bashi wayarsa ya kara daga hankalin al’umma a kan girman matsalar wadda har za a iya cakawa soja wuka har lahira.

Sojan Laftanar Kwamanda M. Buba ya tsaya ne a bakin gadar Kawo, Kaduna domin ya yi facin tayar motarsa a inda barawon ya samu sa’a ya caka masa wuka lamarin da duk da jama’a sun kawo dauki sun yi wa barawon kisan gilla, tuni hukumar kwalejin horas da hafsoshin soji da ke Jaji in da sojan ke karbar horo suka kama mutane 27 a maboyar su.

A Gombe matashin magidanci, Ahmad Kasiran ne masu kwacen waya suka raba da duniya a kan wayarsa lamarin ya daga hankalin jama’a tare da girgiza su.

A yayin hada wannan rahoton wakilin mu ya samu rahoton yadda masu kwacen waya suka cakawa wani malamin jami’a wuka a Kano suka bar shi a cikin jini.

Gagarumar matsalar kwacen waya ta ta’azzara ne a dalilin rashin madafa a halin  tsadar rayuwa. Rashin aikin yi ya mamaye ko’ina ta yadda jama’a ba su samun ayyukan yi. Hauhawar farashin kaya da karyewar darajar naira ya kara girman wannan matsalar wadda ta jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya a cikin fatara da bude kofar ta’addanci da rashin tsaro.

A bisa ga wannan a yau jama’a da dama sun zabi kwacen waya a matsayin hanya mafi sauki ta samun kudi a bisa ga bukatar da ake da ita ta wayoyin da ba sababbi ba.

A haka wasu na ganin mafita ita ce dokar agajin gaggawa, gyaran dokoki, karfafa hanyoyin fasahar bin diddigin gano waya, zartas da hukunci mai tsauri da aiwatar da shiraruwan rage matsalar rashin ayyukan yi.

Inganta dokokin hukumomin tsaro ya zama wajibi kuma hanya ta farko a fafutukar kawar da wannan matsalar. Hobbasar Rundunar ‘Yan Sanda ba mai yawa ba ce domin rahoton hukumar kididdiga ya nuna kashi 90% na wadanda aka yi wa kwacen waya sun kai rahoton faruwar lamarin, amma kashi 11.7% ne kawai aka gano.

A mabambantan ra’ayoyin jama’a da LEADERSHIP Hausa ta tattaro sun bayyana wajibcin gwamnati da musamman hukumomin tsaro da su kaddamar da dokar daukin gaggawa, tare da hukunci mai tsauri kan masu kwacen waya da ke addabar al’umma tun kafin lamarin ya kara tabarbarewar da zai fi karfin hukuma.

“Wajibi ne hukumomin tsaro su kara daura damarar yaki da barayin waya domin matsalar ta wuce duk yadda ake tunani haka ma gwamnatoci su ba da cikakken goyon baya musamman a kafa dokar ta baci domin duk matsalar da ake yi wa jama’a kisan gilla to gagaruma ce haka ma a yaki matsalar shaye- shaye wadda ita sila.” In ji Kallamu Abubakar.

Abba Fadi ya bayyana nasa ra’ayin yana cewar “Inna lillahi wa Inna ilaihi Raji’un. Wannan masifa ni wallahi har na gaji da jin labarin kashe- kashen all’umar Annabi da masu kwacen waya ke yi. A gakiya ya kamata gwamnati ta tashi tsaye a kan lamarin nan tun kafin barayin waya su ci mu da yaki a kasar nan. Idan an kama barayin waya a rika zartar musu da hukuncin kisa a bainar jama’a don ya zama izina ga masu aikatawa.”

A ra’ayin Abdulkadir Aminu ya na ganin domin magance wannan matsalar shine “A dauki matakin kafa dokar ta baci ta hanyar ba- sani ba- sabo a kan barayin waya a kuma tsaurara hukunci ga duk wanda aka kama da kwacen da kuma sayen wayoyin sata.”

Shi kuwa Umar Albashir cewa ya yi “Tabbatar da hukunci ga duk wadanda aka kama da satar waya shine zai magance matsalar da sauran matsalolin da ake fuskanta. Wani babban abin dubawa shine matsalar shaye- shaye ita ce ta haddasa matsalar daba wadda kuma ta haifar da ta’addanci wanda shi kuma ya haifar da sace- sace da kwace- kwace wanda matukar ba a kawar da hanyar shaye-shaye ba to ba a dauki hanyar magance matsalolin ba.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa
Manyan Labarai

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Manyan Labarai

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026

October 7, 2025
Next Post
Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma

Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version