Masu ruwa da tsaki sun yi kira da gwamnatin tarayya da ta lasta rajistar inshorar lafiya ga duk al’ummar Nijeriya, matsayin hanya da za ta taimaka wajen musamman wajen kawo karshen mutuwar yara da suke kasa da shekara biyar.
Gwamnatin Nijeriya da masu ruwa da tsaki ta bangaren kula da lafiya a shekarun da suka gabata sun bullo da tsare- tsaren da za su inganta lafiyar kananan yara a Nijeriya, amma duk da haka ita ce jagora idan ana maganar mutuwar yara ‘yan kasa da shekara biyar a duniya.
- Yadda Daruruwan Dubban Jama’a Suka Halarci Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass Karo Na 37
- Burina Na Zama Tauraro A Harkar Waka A Kannywood — Jibrin
Alal misali hukumar lafiya ta duniya da nahiyar Afirka sun kiyasta kashi 42 na kananan yaran da suke mutuwa abin yana faruwa ne a kasashen da kananan yara da suka kai 857,899 da suke kasa da shekara biyar a kasasr Nijeriya ce abin ke faruwa.
Rahoto ya nuna babbar matsalar da take sanadiyar mutuwar yara ‘yan kasa da shekara biyar a Nijeriya abin ya hada da matsalolin lafiya da suke damuwar kananan yara, musamman ma Jarirai sabuwar haihuwa;( kashi 22.9) cutar mashako (kashi19.4), gudawa (13.2 ), zazzabin maleriya ( kashi13.9 ),sankarau (kashi5.45), rashin kayayyakin abinci masu gina jiki rashin nau’oin abincin da suka kamata kashi (2.8), bakondauro (kashi 2.5), cutar kanjamau/tsida (kashi2), tarinfuka (kashi1.4), sauran cututtukan da ake dauka ta jima’i (kashi1.6.).
Masu ruwa da tsakin suna da tabbacin cewar idan aka yi amfani da tsarin inshorar lafiya ya kasance na kowa da kowa, irin wadannan masu kashe kananan yara masukasa da shekara biyar a kasa baki daya.
Ba abin mamaki ba ne domin al’amarin inshorar lafiya wata hanya ce ta tabbatar da samun kula da lafiyar al’umma yadda ya dace, saidai kuma abin takaici ne saboda yadda ake kulawa da lafiyar kananan yara har yanzu abin babu wani cigaba.
Alal misali a shekarar 2021 an yi wani bincike daya nuna kananan yara wadanda suke kasa da shekara biyar 845 ne wadanda suke kashi 2.7 daga cikin yara 30,804 da suke kasa da shekara biyar,yara 804 wadanda suke samun gajiyar tsarin kula da inshorar lafiya.
Har ila yau binciken ya sake nuna Jihohi wadanda suke da mafi kankantar kananan yara kasa da shekara biyar da suke samun kula da lafiyarsu, yadda ya dace ayi, Jihar Kebbi ce ke da karamin yaro daya wanda ake kulawa da lafiyar shi kamar yadda yakamata daga cikin kananan yara 1,030 da aka gano su cikin binciken da aka yi akansu.
Jihar Taraba tana da yara biyu kacal da suke amfana da tsarin kula da lafiyar inshorar lafiya daga cikin kananan yara ‘yan kasa da shekara biyar 628, Jihar Abia na da yara biyu ne da suke cin gajiyar tsarin inshorar lafiya ta kasa daga cikin kananan yara485.
Jiha kamar Legas tana da kananan yara 137 masu amfana daga shi tsarin,wanda shine kashi 7.9 daga cikin 1,743 yayin da Jihar Delta tana da kananan yara 124 wanda shine kashi 19.9 na cikin kananan yara 623 wadanda aka gano bayan shi binciken da aka yi.
Inganta tsarin kula da lafiya hukumar kula da inshorar lafiya ta kasa NHIA
Masu ruwa da tsaki a bangaren kula da lafiyar al’umma kamar yadda yakamata ko ake tafiyar da tsarin a kasashen da suka cigaba, sun yi kira da taimakawa duk ‘yan Nijeriya da suka hada da masu ruwa da tsaki,a harkar kula da lafiyar al’umma.Wannan kuma domin aiwatar da shi tsarin kula da lafiyar al’umma na inshorar lafiyar abinda ya zama dole,kamar yadda dokar kafa hukumar inshorar lafiya ta kasa domin cimma muradun kula da lafiyar al’umma yadda ya dace.
Mataimakiyar Jnar Manaja har ila yau mai kula da ofishin Jihar Legas na hukumar NHIA, Mrs Aisha Haruna Abubakar, tayi hira da jaridar LEADERSHIP,a taron wayar da kai wanda aka yi ma kungiyar maruba labarum lafiya ta kasa (HEWAN) a LegasTa bayyana cewa dalilin kafa hukumar inshorar lafiya ta kasa dokar ta shekarar 2022 shine bayar da damar kulawa da lafiyar duk ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da inda suke zama ba, ko masu Attajirai ne ko Fakirai.