An yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano mai jiran gado akan ta yi kokari wajen hana algus da karin farashin kaya na ba gaira ba dalili da ‘yan kasuwa suke ta kawo tsarin kayyade farashi.
Dan takarar Gwamnan jihar Kano na jam’iyyar ZLP a zabenda ya gabata. Alhaji Isah Nuhu Isah ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.
- Na Yi Mamakin Ganawar Antony Blinken Da Tinubu -Atiku
- Sin Ta Samar Da Tallafin Jin Kai Na Gaggawa Sama Da 800 Ga Kasashen Waje Cikin Shekaru 5
Ya ce sun so da Allah ya basu nasara a jam’iyyar ZLP su kawo gyara a irin wadannan abubuwa, saboda gwamnati na ko in kula da yan kasuwa, kowa abinda ya ga dama yake ba kayyade farashi kuma an zura ido gurbatattu sun shiga kasuwa suna yin algus a kayyaki.
Ya kamata gwamnati ta zuba ido a irin wadannan abubuwa ta duba sosai ta ga yanda ake gallazawa al’umna a rage radadin rayuwa, duk da abune mai wahala, amma yakamata ace gwamnati ta shigo an sami sauki.
Ya ce abin takaici kullum ka shiga kasuwa sai kaya ya tashi ba dalili hakannan kawai za’a kara farashi, Dan yana kira gwamnati Allah ya bats nasara ta kawo gyara.
Alhaji Isah Nuhu Isah ya sake kira ga gwamnati ta kula da harka ta tsaro yara sun lalace da shaye-shaye akan dan abu kalilan waya bata kai ta kawo ba za’a tare mutum aji masa rauni har ma ta kai ga kisa.
Dan haka yakamata a dauki mataki na musamman a samar da wani kwamiti da zai rika zagawa da ya kunshi jami’an tsaro dana sa kai dan ganin an kyautata tsaro.
Alhaji Isah Nuhu Isah ya yi fatan Allah ya taya riko ga gwamnati mai zuwa da kuma bata damar yin abinda yakamata dan kyautawa al’umma.