A ranar Asabar ne Babban Kwamandan Makarantar Horas da matsakaitan Hafsoshi ‘Warrant Officers Academy’ Manjo Janar AG Mamuda ya bukaci sojojin Nijeriya su kara jajircewa a wajen gudanar da ayyukansu na tsaron kasa da al’umma.
Janar Mamuda ya bayyana haka ne a matsayin babban bako a taron bikin al’adun gargajiya da sojoji ke yi a duk shekara wanda ake kira da ‘West African Social Activities’ WASA. A wannan shekarar dukkan barikin sojoji da ke yankin Zariya suka hadu a Barikin Depot da ke Sabon Gari Zariya a Jihar Kaduna.
- Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa
- Hukumar JAMB Ta Zuba Naira Biliyan 6 A Asusun Gwamnatin Tarayya A Shekarar 2024
Ya kuma tunatar da su a kan bukatar su zama masu sallamawa, karfin hali da rike gaskiya wajen gudanar da ayyukansu a dukkan lokaci.
A jawabinsa na maraba, Kwamanda Barikin Depot Zariya, Manjo Janar MA Abdullahi ya nemi sojojin da ake a Zariya su kara kaimi wajen gudanar da aikinsu kamar yadda shugaban rundunar sojin Nijeriya ya zayyana a kudurinsa na bunkasa rundunar kamar yadda dokokin kasa ta tanada.
Ya kuma mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka samu halartar bikin. Kungiyoyin al’adun gargajiya na Hausa, Ibo, Yoruba, Tibi da Fulani suka baje kolin su a wajen bikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp