Dandazon ’yan kallo sun halarci cibiyar raya al’adun kasar Sin dake birnin Abuja fadar mulkin Najeriya a ranar Lahadi, inda aka nuna fasahohin kida da wake salon Pingtan, wanda ya samo asali daga yankunan kogin Yangtze, ya kuma game sassan lardunan Jiangsu, da Zhejiang da birnin Shanghai.
Yayin taron na karshen mako, an nuna nau’o’in wasanni a kalla 11, masu kunshe da labaru da ake bayarwa hade da kida na musamman domin gamsar da masu kallo.
Zaman nuna wasan na Pingtan da aka yiwa lakabi da “Wuxi Ballads: Portraits of Watertown” ya hallara jama’a daga sassa daban daban, ciki har da jami’an gwamnati, da masu sana’o’in nuna fasahohi, da malamai da daliban makarantun sakandare na Najeriya, wadanda suka taru don kallon salon ba da labarai hade da kade-kade na kasar Sin, matakin da ya kara daga matsayin musayar al’adu tsakanin Sin da Najeriya. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp