An rabawa iyalan jami’an tsaro na farin kaya (NSCDC) guda bakwai da ‘yan bindiga suka yiwa kwanton bauna a karamar hukumar Birnin Gwari cakin banki da basu damar guraben aiki.Â
An raba masu cakin bankin ne a matsayin tallafi kafin a biya iyalansu hakkokinsu na aiki.
A cikin sanarwar da kwamanda janar na NSCDC Dakta Ahmed Abubakar Audi ya fitar, ya bayyana hakan ne a lokacin da babbar tawaga ta mahukuntan NSCDC ta ta je yiwa iyalan mamatan ta’aziyya a jihar Kaduna.
Sanarwar wadda kakakin NSCDC DCC Olusola Odumosu ya fitar ta ce, Kwamandan ya ce, ba wannan ne karo na farko da muka yi rashin jami’anmu a Birnin Gwari ba, inda kuma ya sanar da biyan kudin diyyar mamatan wanda a yanzu ofis din ministan harkokin cikin gida ke kan maganar.
Ya kuma mika ta’aziyar ministan Rauf Aregbesola ga iyalan mamatan, inda kuma ya gode wa Allah yadda daya daga cikin jami’an SCA Thomas Hassan ya kubuta a lokacin harin na ‘yan bindigar wanda aka duba lafiyarsa a wani asibiti aka kuma sallame shi.