An rantsar da jagoran kuyin mulkin kasar Gabon, Janar Brice Oligui Nguema, a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar.
Nguema, ya jagoranci kifar da gwamnatin shugaba Ali Bongo Ondimba a ranar Laraba da hakan ya kawo karshen daularsa da ke mulki tun 1967.
- Yadda Sojoji Suka Yi Juyin Mulki A Gabon
- An Yi Wa Manyan Hafsoshin Soji Ritaya A Ruwanda Kan Fargabar Juyin Mulki
Janar din na Gabon wanda ya yi rantsuwar kama aiki, bikin da aka gudanar a gaban alkalan kotun tsarin mulkin kasar, ya lashi takobin kiyaye nasarorin dimokuradiyya.
“Na rantse da Allah a gaban al’umman Gabon zan kare kima da martabar demukuradiyya,” Nduema ya shaida.
Ya yi alkawatin cewa zai gudanar da sahihi kuma ingataccen zaben da zarar wa’adin gwamnatin rikon kwarya ya kare, kodayake bai bayyana takamaimai zuwa yaushe ba ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp