A kwanakin baya ne, aka kammala kashi na farko na layin dogo a jihar Lagos dake Najeriya, wanda kamfanin kasar Sin ya gudanar, layin dogo mai amfani da lantarki na farko a yankin yammacin Afirka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kammala aikin zai taimaka wajen daidaita matsalar zirga-zirgar ababan hawa, da saukaka tafiye-tafiye na jama’a da bunkasa tattalin arziki da samarwa kasar kwarewa a aikin zirga-zirgar jiragen kasa da ma ragowar kasashen yammacin Afirka.
Mao Ning ta bayyana cewa, raya shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”mai inganci ya sa kaimi ga bunkasar dukkan kasashe, wadda ta samu maraba daga jama’ar kasashe masu bin shawarar.
A shekara mai zuwa ne, za a yi bikin cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”. Sin tana son yin aiki tare da bangarori daban daban, wajen takaita nasarorin da aka samu, da tsara sabuwar taswira don sa kaimi ga raya wannan shawara, wadda zai amfanawa duniya da jama’a baki daya. (Zainab Zhang)