Rahotanni daga masu shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyar (CIIE) na cewa, an riga an kama kashi 85 cikin 100 na yankin baje kolin kamfanoni da aka shirya gudanarwa a Shanghai.
Mataimakin darektan ofishin CIIE Sun Chenghai, ya shaida wa taron manema labarai Larabar nan yayin da rage kwanaki 100 a bude bikin cewa, sama da kamfanoni 270 daga cikin 500 dake kan gaba a duniya, da manyan masana’antu ne suka tabbatar da halartar bikin baje kolin, wanda aka shirya gudanarwa a birnin Shanghai daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba.
Sun Chenghai ya bayyana cewa, wasu kamfanoni daga cikin 500 dake kan gaba a duniya da suka hada da Rio Tinto, da BHP Billiton da Gileyad, za su halarci bikin ne a karon farko.
Sun ya kara da cewa, don rage tasirin annobar COVID-19 da rashin tabbas kan tattalin arzikin duniya kan kananan da matsakaitan masana’antu da za su halarta, bikin baje koli na CIIE ba kawai zai inganta daidaita manufofin tallafi kamar tallafin haraji da saukakawa ayyukan kwastam ba, har ma zai ba da karin rumfuna kyauta ga kamfanoni daga kasashe masu karamin karfi.(Ibrahim)