An rufe babban taron wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan jarjejeniyar Ramsar kan yankuna masu dausayi ko COP14 a takaice a jiya Lahadi, inda aka fitar da “Sanarwar Wuhan”, da “Tsare-tsaren kare yankuna masu dausayi a fadin duniya tsakanin shekarar 2025 zuwa 2030”, tare kuma da cimma wasu muhimman sakamako da dama.
Bisa matsayinta na kasa mai shugabancin taron, kasar Sin ta gudanar da ayyuka daban daban yadda ya kamata, kuma duk wadannan sun taimaka wajen babban sakamakon da aka cimma a yayin taron, lamarin shi ma ya nuna karfin tasirin kasar Sin a duniya.
Kana babban taron ya tsai da kuduri cewa, za a kira babban taron COP15 a kasar Zimbabwe. Haka zalika, an kira taron zaunannun mambobin kwamitin yarjejeniyar karo na 61 bayan rufe taron, inda aka zabi kasar Sin da ta zama shugabar kwamitin, domin jagorantar ajandar yarjejeniyar cikin shekaru uku masu zuwa. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)