Yanayi na matsanancin zafi ya tilasta wa mahukuntan Sudan ta Kudu rufe makarantu a fadin kasar don kaucewa hatsarin da ke tattare da yanayin, duba da yadda ya ke ci gaba da ta’azzara.
Rahotanni sun ce masana yanayi sun tabbatar da cewa nan da makonni masu zuwa kasar za ta tsinci kanta cikin tsananin zafin da ba ta taba ganin irin sa a tarihi ba.
- Dole Ne A Hukunta Wadanda Suka Kashe Sojoji A Delta – Tinubu.Kasuwar Sin Na Taimaka Dunkule Tattalin Arzikin Duniya
Ma’aikatar ilimi da ta lafiya sun yi hadin gwiwa wajen shawartar iyaye da su yawaita zuba wa yaransu ruwa a jiki tare da killace su a gida ba tare da barin su shiga rana ba.
Gwamnatin kasar ta yi barazanar karbe lasisin duk makarantar da aka samu a bude lokacin wannan tsananin zafi, sai dai kuma ba ta yi karin haske kan lokacin da za a bude makarantun ba.
Masana yanayi sun alakantan tsananin zafin da karancin ruwan sama, sauyin yanayi da kuma fari da kasar ke fama da shi.