An rufe taron koli na kafofin yada labarai wanda aka yi a karon farko dangane da kwaikwayon hazikancin dan Adam a Afrika, jiya Laraba a Yaounde, hedkwatar Kamaru. Kungiyar masu gidajen rediyo ta Afirka wato AUB da UNESCO ne suka yi hadin gwiwar gabatar da wannan taro mai wa’adi kwanaki 3 bisa taken “Kwaikwayon Hazikancin dan Adam-sabuwar makomar kafofin yada labarai a Afrika”.
Bisa gayyatar AUB, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta tura tawagarta zuwa Yaounde don halaratar taron, inda ta zama kafar yada labarai daya tilo da ta gabatar da jawabi a bikin budewa. Da take jawabi, darektar hukumar CMG a Afrika Song Jianing ta yi bayyani kan yadda CMG take kokarin samun ci gaba wajen ingiza kafa tsarin “5G+4K/8K+AI” da nazarin kwaikwayon hazikancin dan Adam da sauran kimiyya da fasahar kirkire-kirkire.
- Xi Ya Jaddada Zurfafa Gyare-gyare Don Inganta Kwarewa A Sabbin Fannoni
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Makiyayi Da Shanu 35 A Wani Sabon Harin A Filato
CMG ta kafa rumfa yayin bikin, inda ta gabatar da sabbin fasahohin kirkire-kikiren da take amfana da su a cikin ayyukanta, abin da ya ja hankalin mahalarta taron sosai.
Babban jami’in gudanarwa na kungiyar AUB Grégoire Ndjaka ya jinjinawa fasahohin da CMG ke amfani da su. Yana mai fatan kafofin yada labarai na Afrika za su koyi basirar Sin duba da bunkasuwa cikin sauri da ci gaban da take samu a fannin kimiyya da fasaha da kwaikwayon hazikancin dan Adama da sauransu. (Amina Xu)