Wani sabon bincike da aka gudanar kan lamarin da ke wakana a fannin arzikin man Nijeriya, ya nuna cewar, an fitar da ganga sama da miliyan 17 na danyen mai daga kasar nan zuwa kasashen ketare ta barauniyar hanya, a tsakanin 2016 zuwa 2020.
Rahoton da Andrew Ogochukwu Onwudili, babban jami’i mai binciken kudi na Nijeriya, ya fitar, ya kiyasta cewar kwatankwacin kudin danyen man fetur din da a iya cewa an sace daga kasar nan ya kai Dala Tiriliyan daya da biliyan 20, da miliyan 969 da dubu 281.
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tsohon Gwamnan Imo Hari, Sun Kashe ‘Yansanda 4
- ‘Yan Bindiga Sun Sake Afkawa Garin Jere Sun Yi Awon Gaba Da Mutane
A cikin rahoton, an tuhumi Ofishin Akanta-Janar na gwamnatin Nijeriya da laifin biyan sama da Naira biliyan 73 ga jami’an da suke tantance inganci da adadin albarkatun mai da isakar gas din da ake shirin fitar da su daga kasar nan.
Mai binciken yadda ake kashe kudaden Nijeriya, ya bayyana cewar, kudaden da aka biya ba tare da an yi kasafinsu ba, ya saba wa tanadin doka a sashe na 80(4) na kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999.
Tsohon babban mai binciken kudi, Adolphus Agughu ne, ya sanya hannu kan rahoton, aka kuma mika kundin ga magatakardar majalisar dokokin Nijeriya a ranar 29 ga Yuni, na shekarar da ta gabata.
Nijeriya dai na ci gaba da yaki da masu satar man fetur ta hanyar fasa bututun mai.
Hakan dai na sanya gwamnati asarar maduden kudade marasa adadi.