Dan wasan gaban Nijeriya da Galatasaray Victor Osimhen na daga cikin ‘Yan wasan da aka zaɓa domin samun kyautar gwarzon Dan wasan kwallon kafa na bana da hukumar kwallon kafa ta Afirika (CAF) ta ke bayarwa duk shekara. Osimhen ne ya lashe kyautar a shekarar 2023 yayin da Ademola Lookman ya lashe a shekarar da ta gabata.
Yau Laraba, CAF ta fitar da sunayen mutum 10 wanda a cikinsu ne za a zabi Wanda za a bai wa kyautar ta bana, sunayen manyan ‘yan wasan Afirka ne suka cika jadawalin ‘yan wasan, daga ciki akwai Muhammad Salah (Liverpool/Egypt), Achraf Hakimi (PSG/Morocco), Seydou Guirassy (Borrusia Dortmund/Guinea).
Sauran sun hada da Fiston Mayele (Congo), Oussama Mayoulai (Morocco), Frank Anguissa (Cameroon), Denis Bouinga (Gabon) da Ndiaye da Pape Sarr na Kasar Senegal, Osimhen wanda ya lashe kyautar a shekarar 2023 ya buga kakar wasa mai kyau tare da Galatasaray wadda ya taimakawa ta lashe gasar Turkiyya yayin da ya zura kwallaye 26.