Jama’a sun fito kamar yadda ya kamata domin kada kuri’a a zaben kujerar gwamna da ‘yan majalisar dokokin jiha, da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke gudanarwa a jihar Adamawa.
Mazabar Ajiya 001 da 003, a karamar hukumar Yola ta arewa da Makama A, 002, Lamido Aliyu Mustahpa, dake karamar hukumar Yola ta kudu, su na daga cikin cibiyoyin da LEADERSHIP HAUSA, ta ziyarta, zaben yana gudana lami-lafiya.
Haka kuma rahotanni daga sassan jihar da dama wuraen da’ake gudanar da zaben sun tabbatar da cewa komai na tafiya kamar yadda aka tsara, sai dai an samu jinkirin kai kayan aikin zabe kan kari a wasu cibiyoyin.
A bangare guda kuwa, jam’ian tsaro sun tsaurara matakan tsaro, musamman a Yola fadar jihar, inda wasu daga manyan hanyoyin garin an dakilesu, haka kuma garin bashiga babu fito.
Haka kuma a cikin garin Yola da Jimeta, jama’a su na gudanar da harkokinsu na yau da kullum, kasuwanni da dama abude su ke.