Babban bankin Nijeriya (CBN), ya ce an samu haɓakar tattalin arziƙin ƙasar nan da kashi 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024, da muke ciki wanda hakan ya zarce kashi 3.19 a rubu’i na biyu na shekarar.
CBN ya bayyana haka ne cikin rahoton da ya fitar wanda ya alaƙanta wannan ci gaban da wasu ɓangarorin daban-daban da na albarkatun man fetur, inda ya ƙara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya ragu a ɗan tsakankain.
- Kamfanin Jiragen Sama Na Azman Ya Musanta Zargin Sayar Da Jiragensa Ga Iran
- Bukukuwan Kirismeti: Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Iyalan Waɗanda Suka Rasu Sakamakon Turmutsitsi A Wasu Jihohi
Kan batun man man fetur, kuwa rahoton CBN din ya ce adadin ɗanyen man da Nijeriya, ke fitarwa ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.33, fiye da ganga 1.27 da ake fitarwa a baya.
Hakan ya ce yana da nasaba da ingancin rsaro da aka samu a lyan watannin baya-bayan nan musamman a yankin Neja Delta, da ma ƙoƙarin gwamnati wajen inganta harkokin kasuwanci a cikin gida da ƙasashen ƙetara.