Hauhawan farashin kayan masarufi na ci gaba da karuwa fiye da kima, inda ya haura zuwa kashi 28.92 a watan Disamban 2023, wanda hakan na nuni da cewa a sama da shekaru 24 Nijeriya ba ta taba fuskantar irin wannan hauhuwar farashin ba.
A cikin rahoton da hukumar kiddigga ta kasa (NBS) ta fitar a makon nan, ta ce zuwa watan Disamban shekarar da ta gabata, hauhawar farashi ya karu zuwa kashi 28.92 daga kashi 28.20 a watan Nuwamba 2023.
- Hadin Abincin Kajin Gidan Gona Masu Saurin Girma
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Tawagar Amurka Ta Rukunin Ayyukan Hada-hadar Kudi Na Sin Da Amurka
Rahoton ta ce, hakan ya nuna an samu karuwa hauhawar farashi da tazarar 0.72 daga watan Nuwamban kawai.
Hukumar kididdiga ta ce hakan ta faru ne sanadin tsadar farashin abinci, lamarin da kuma ya ta’azzara tsadar rayuwa da karin matsin lamba kan babban bankin Nijeriya da ya yi wajen kara kudin ruwa.
Hukumar ta ce idan aka duba kididdigar hauhawa a Disamban 2022 da ya kai zuwa 21.24 kuma aka kwatanta da na shekarar 2023, za a iya cewa duk shekara Nijeriya na samun karuwar hauhawar farashi.
Hukumar ta ci gaba da cewa hauhawar farashin abinci zuwa Disamban 2023 ya kai kaso 33.93 cikin 100 a shekara guda, kaso 10.18 na hauhawa idan aka kwatantanta da na Disamban shekarar 2022 mai kashi 23.75 cikin dari.
Ta ce, hauhawar farashin ya faru ne sakamakon tsadar kayan abinci irin su buredi, man fetur da man girki, dankali, doya, kayan hatsi, kifi, nama, kayan marmari, madara, kwai da dai sauran kayan abincin da ake amfani da su a Nijeriya.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa al’ummar Nijeriya na ci gaba da nuna damuwarsu kan yadda kayan masarufi ke tashin gwauron zabi, lamarin dai ya kara jefa jama’an kasar cikin matsatsi da kuncin rayuwa. Duk da cewa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu na ikirarin nemo hanyoyin fita daga matsatsin da ake ciki musamman na tattalin arziki da sauransu.
Masharhanta irinsu, Dabid Omojomolo na cibiyar ‘Caital Economics’ sun yi hasashen cewa hauhawar farashi a Nijeriya za ta iya kai wa har kashi 30 nan da karshen wata uku na farko wannan shekara.
A cikin watan Mayu ne Shugaba Tunubu ya bijiro da gyare-gyare mafi karfin hali a cikin shekaru gomma bayan ya yi watsi da manufar cire tallafin man fetur, darajar kudin Nijeriya kuma ta karye a kokin farfado da bunkasar tattalin arziki.