Zuwa karshen watan Yulin bana, kamfanoni sama da miliyan 1.5 na yankin Hong Kong na kasar Sin ne suka yi rajista a yankin, yayin da sama da kamfanoni 15,000 da ba na yankin ba, su ma suka yi rajista.
Jagoran yankin Hong Kong John Lee ne ya bayyana haka jiya, inda ya ce dukkan adadin ya kai matakin koli.
- Masana Kimiyya Na Sin Sun Samar Da Fasahar Sa Ido Kan Cututtukan Da Ake Samu Daga Sauro
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15
Cikin wani bidiyon da aka wallafa a shafin sada zumunta, John Lee ya ce, daga Janairun 2023 zuwa Yulin 2025, shirin neman zuba jari a Hong Kong, ya taimakawa kafuwar kamfanoni 1,333 ko kuma fadada ayyukansu a yankin, lamarin da ya samar da jarin dalar Hong Kong miliyan 174, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 22.17, a jarin da aka zuba kai tsaye a rabin farko na bana tare da samar da guraben aikin yi sama da 19,000
Lee ya kara da cewa, fifikon musammam da Hong Kong ke da shi karkashin manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu’, ya ba yankin damar jan hankalin masu zuba jari na ketare domin su lalubo damarmakin kasuwanci a yankin da ma kasuwar babban yankin kasar Sin tare da taimakwa kamfanonin babban yankin shiga kasuwannin ketare.
Bugu da kari, ya ce kamfanonin waje da dama sun samu damarmakin kasuwanci a Hong Kong, kuma suna ci gaba da fadada harkokinsu. Su ma kamfanonin babban yankin kasar Sin sun aminta da karfin Hong Kong kuma suna hada gwiwa da tawagar dake Hong Kong wajen lalubo damarmakin dake akwai a kasuwanni masu tasowa na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp