An ga karuwar adadin matafiya a dukkan sassan kasar Sin a rana ta farko na hutun kwanaki 3 na bikin sharar kaburbura na na Qingming na kasar Sin a bana, inda dukkan hanyoyin sufuri suka ba da rahoton samun karuwar matafiya.
Ma’aikatar kula da sufuri ta kasar Sin ta ce, a ranar 4 ga watan Afrilu, watau rana ta farko na hutun, an yi tafiye-tafiye sama da miliyan 20.9 ta jiragen kasa, adadin da ya karu da kaso 8.4 a kan na bara.
- An Kori Jirgin Ruwan Japan Da Ya Shiga Yankin Ruwan Kasar Sin Ba Bisa Ka’ida Ba
- Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta
Adadin tafiye-tafiyen da aka yi ta ruwa kuwa, ya kai 880,000, karuwar kaso 24.4 yayin da na jiragen sama ya kai kusan miliyan 1.79, karuwar kaso 8.6.
Adadin tafiye-tafiyen da aka yi ta motoci ya dauki kaso mai yawa na jimilar bulaguron, inda ya kai miliyan 264.72, karuwar kaso 9.7 kan na bara. Haka kuma, karin mutane na tafiye-tafiye cikin motocinsu na kansu, inda adadin ya kai miliyan 228.23 a ranar Juma’a, karuwar kaso 11.1.
A bana, bikin ya fado ne a ranar 4 ga watan Afrilu. Biki ne na gargajiya da Sinawa ke girmama mamata. Haka kuma bikin na samar da wata dama ga mazauna Sin su gudanar da yawon bude ido ko wasu harkokin nishadi. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp