Sabon yankin cinikayya na kasa da kasa da ya hada yankunan kasa da teku, wanda ke zaman muhimmiyar tashar jigila da ta hada yankin yammacin Sin da kasuwannin ketare, ya yi jigilar kwantainonin 209,000 ta hanyar jiragen kasa da teku, cikin watanni biyu na farkon bana.
A cewar kamfanin kula da jiragen kasa ta Nanning ta kasar Sin, adadin ya zarce jimilar ta shekarar 2019, inda aka samu karuwar kaso 58.4 a kowacce shekara.
- Fitaccen Fim Din Na Kasar Sin Mai Suna “Ne Zha 2” Ya Zama Na 7 A Jerin Fina-finai Mafi Samun Kudi A Duniya
- Zargin Neman Yin Lalata: Ina Da Kwararan Hujjoji Akan Akpabio – Natasha
A watan Fabreiru, bukatar jigilar kayayyaki ta karu, inda aka samu karuwar jigilar kayayyaki kamar na katako da da duwatsu, daga yankin Guangxi Zhuang mai cin gashin kansa na kudancin kasar Sin da kuma ganyen shayi da takardun Roll Paper daga lardin Hunan na tsakiyar kasar.
Tashar mai cibiya a birnin Chongqing, ta hada tashohin ruwa na kasa da kasa da layukan dogo da hanyoyin ruwa da tituna, inda ta ratsa lardunan Guangxi da Yunnan dake kudancin kasar Sin.
Yanzu hidimar jigilar kayayyaki ta mamaye wurare 158 a fadin birane 73 na cikin gida, kana ta mika zuwa tashoshin ruwa 556 a kasashe da yankuna 127. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp