Hukumar kula da shige da ficen jama’a ta kasar Sin ko NIA, ta ce adadin tafiye tafiye a ciki da wajen kasar sun kai miliyan 2.07 a duk rana, yayin hutun bikin Qingming na kasar Sin da ya gabata, adadin da ya nuna karuwar kaso 19.7 bisa dari a shekara.
Hukumar ta NIA ta ce yayin hutun na kwanaki 3 wanda aka fara tun daga ranar Juma’a 4 ga watan nan na Afirilu, jami’an lura da kan iyakokin kasar Sin sun tantance zirga-zirgar matafiya ta kan iyakokin kasar har miliyan 6.21.
Kazalika, wadannan tafiye-tafiye sun hada da na baki ‘yan kasashen waje har 697,000, adadin da ya karu da kaso 39.5 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar 2024. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp