An yi gagarumin bikin murnar cika shekaru 70 da kafa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai a birnin Urumqi jiya Alhamis 25 ga watan Satumban nan, inda aka nuna wa duniya manyan nasarorin tarihin da jihar ta samu a cikin shekaru 70 da suka gabata, da kuma tabbatar da fifikon tsarin yankunan mabambantan kabilu masu zaman kansu na kasar Sin, gami da sakamako mai gamsarwa wajen aiwatar da manufofin tafiyar da harkokin Xinjiang da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ke yi a sabon zamani, tare kuma da shaida babbar niyyar da al’ummun jihar Xinjiang ke da ita a fannin raya jiha mai tsarin gurguzu, kuma irin ta zamani, karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin.
Kwarewar gwamnatin kasar Sin wajen tafiyar da harkokin mulki, abu ne da yake a bayyane, al’amarin da ya zama babban dalilin da ya kawo manyan sauye-sauye ga jihar ta Xinjiang. Sakamakon matukar kokarin da aka yi, an cimma nasarori da dama wajen dakile ’yan a-ware na wurin, har ta kai ba a samu wakanar ayyukan ta’addanci a tsawon shekaru da dama a yankin ba, al’amarin da ya tabbatar da kwanciyar hankali, da hadin-kan mabambantan kabilun yankin.
Zaman karko shi ne ke haifar da tabbaci ga ci gaban tattalin arziki. Ci gaba mai inganci da jihar Xinjiang ta samu, zai taimaka gaya ga ci gaban sauran kasashe, tare da samar da damarmakin zamanintar da yankin tsakiyar Asiya gami da sauran shiyyoyi.
A halin yanzu, kasar Sin na himmatuwa wajen zamanintar da kanta bisa salon musamman, yayin da aikin zamanintar da jihar Xinjiang ma ke cikin sabon mafari. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kafa alkiblar ci gaban Xinjiang a nan gaba, ciki har da raya sana’o’i na musamman, da bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da raya al’adu da sana’ar yawon shakatawa tare, da inganta aikin kiyayewa, gami da farfado da tsarin muhallin halittu, da gaggauta raya muhimmin yankin tattalin arziki dake kan hanyar siliki da sauransu.
Gagaruman sauye-sauyen da jihar Xinjiang ta samu sun shaida cewa, yadda jama’a ke more rayuwa, hakkin dan Adam ne mafi muhimmanci. Babu shakka, jihar Xinjiang tana fuskantar makoma mai haske. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp