A ranar 16 ga watan nan, wato gabannin bude taron kolin kasar Sin da kasashen Tsakiyar Asiya, aka samu nasarar gudanar da taron tattaunawa tsakanin kafofin yada labaru na sassan biyu a nan birnin Beijing, wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG ya jagoranci shiryawa, kana manyan kafofin yada labaru na kasashen yankin Tsakiyar Asiya 5 suka halarta.
A yayin taron, jami’an CMG, da manyan kafofin yada labaru na kasashen yankin Tsakiyar Asiya, da jakadun kasashen yankin Tsakiyar Asiya a kasar Sin, da masana, sun yi musayar ra’ayoyi dangane da taken taron, wato “zamanantarwa irin ta kasar Sin da kasashen Asiya ta Tsakiya, kana da sabon ci gaba da sabbin damammaki”, sun kuma tattauna sabon nauyi da ke bisa wuyan kafofin yada labaru, dangane da aikin zamanantarwa.
Dukkan mahalarta taron na ganin cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin, ta samar wa bil Adama sabon zabi, ta kuma samar da abin koyi ga kasashe masu tasowa, ciki had da kasashen yankin Tsakiyar Asiya, wadanda ke kokarin zamanantar da kansu bisa dogaro da kansu. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp