Kwanan nan ne aka rufe babban taron duba yarjejeniyar haramta amfani da makamai masu guba karo na 9 a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Litinin cewa, taron gami da nasarorinsa sun shaida cewa, an cimma tudun-dafawa wajen tabbatar da tsaron halittu a duniya, al’amarin da ya dace da babbar moriyar kasa da kasa, kuma kasar Sin ta yi maraba da hakan.
Tabbatar da tsaron halittu ba shi da iyaka. A shawarar da ta shafi tsaron duniya da ya gabatar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ya dace a tsaya ga kiyaye tsaro a bangarori daban-daban, da shawo kan batutuwan da suka shafi tsaron halittu cikin hadin-gwiwa.
Kasar Sin ta nuna kwazo wajen halartar babban taron a wannan karo, inda kuma ta taimaka sosai wajen cimma wasu takardu, tare da gabatar da wasu shawarwari, ciki har da tabbatar da mutunta yarjejeniyar ta hanyar kafa tsarin bincike, da kara raya fasahohin halittu ta hanyar lumana, don su amfani kowa da kowa da sauransu, abun da ya bayyana niyyar kasashen da suka daddale yarjejeniyar, musamman kasashe masu tasowa.
(Murtala Zhang)