Jami’an tsaro sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sha biyu (12) a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi ciki har da wani shugaban masu garkuwa da mutane Madaki Mansur wadanda suka addabi al’umma a yankin da jihohin makwabta Gombe, Taraba da jihar Filato.
A wata sanarwar da Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Litinin ya ce, “A ranar 19 ga watan Disamban 2022 hadakar jami’an tsaro sun yi arangama da wadanda ake zargi ‘yan bindiga ne da masu garkuwa da mutane a maboyarsu daban-daban guda hudu da ke Mansur, Digare, Gwana da kuma Dajin Madam a karamar hukumar Alkaleri.”
Ya yi bayanin cewa a bisa shan karfinsu da jami’an tsaron suka yi, a kalla sha biyu daga cikin ‘yan garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ne suka rasa rayukansu a musayar wutan da suka fafata inda wasu kuma suka arce da harbin bindiga a jikinsu, “Kuma an tarwatsa su daga sansaninsu.”
Wakil ya ce sun kwato makamai, babura da sauransu a wajen da aka fafatan. Ya kuma nanata cewa za su cigaba da kokarinsu na dakile aniyar ‘yan ta’adda a fadin jihar.