Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ruwaito ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar na cewa, an samu sabbin nasarori a hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, a shekarar da ta gabata.
Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2022, cinikayyar kayayyaki da Sin ta yi da kasashen dake kan hanyar, ya kai yuan triliyan 13.8, wanda ya karu da kaso 19.4 a kan na shekarar da ta gabace ta.
Har ila yau, yawan kayayyakin da Sin ta fitar da wadanda suka shigo kasar, sun kai yuan triliyan 42, wanda ya kai matsayin koli a shekarar 2022. Kasar Sin ta rike kambunta na kasancewa kan gaba a fannin cinikayyar kayayyaki cikin shekaru 6 a jere. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)