Akwai isassun jami’an tsaro a rumfunan zabe a wuraren da ake yin zabe a kananan hukumomin Birnin Kebbi, Kalgo da Sauran su.
Jami’an tsaro daga sojoji, ‘yan sanda, Civil Defence, Hukumar Shige da Fice, NDLEA da dai sauran su na nan a kowane muhimmin yanki na rumfunan zabe.
A yayin da wakilinmu ya aiko da rahoto kan rumfunan zabe da ake gudanar da zabuka a rumfar zabe ta 015, da ke a babbar kotun shari’a a garin Ambursa, rukunin zabe 021, Kardi Service Centre, rumbun zabe 005, Boyi Mai Rake Takalau da Garkar Hikimi Takalau.
Haka kuma makarantar Government Day Secondary School, Kalgo, rumfar zabe 009, Wuro Gauri, da Badariya Gari, Hirishi Gari, dukkansu a kananan hukumomin Kalgo da Birnin Kebbi, jami’an tsaro sun tsaya tsayin daka a wurare daban-daban a rumfunan zabe yayin da ake ci gaba da kada kuri’a.
Wakilinmu ya kuma ruwaito cewa, ana sintiri sosai da jami’an tsaro a yankunan da ake gudanar da zabe a yau. ‘Yansanda, Sojoji, DSS da dai sauransu na sintiri a motocinsu na da motocin sojoji suna zagayawa. Hakazalika, akwai É—imbin fitowar masu jefa Æ™uri’a mata da maza cikin tsari. Haka kuma an fara kada kuri’a daidai karfe 8:30 na safe ba tare da korafe korafe ba.