Shugaban Amurka Donald Trump tare da shugabannin Masar da Katar da Turkiyya sun sanya hannu kan kashi na farko na yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza a wurin shakatawa na Sharm el Sheikh da ke Masar.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a gaban shugabannin kasashen duniya fiye da 20 wadanda suka halarci taron.
- Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya
- Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn
Yarjejeniyar ta kawo karshen yakin Gaza, wanda hakan ya zamo abu mai matukar tarihi ga shugaba Trump da kuma shugabannin kasashen yankin.
Yanzu kuma za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da sauran sharuddan da ke ke kunshe a yarjejeniyar.
Masu sanya ido na ganin cewa aikin sake ginan yankin Gaza wanda aka rushe kusan daukacinsa a yakin da aka yi na shekara biyu, zai zama babban kalubale.
Wannan ce ranar da kowa ke jira -Trump
A lokacin da Donald Trump ya yi jawabi, ya bayyana yau a matsayin “ranar da kowa ya yi ta hankoro da addu’ar ganin zuwan ta.”
Shugaban na Amurka ya ce “Wannan yarjejeniya mai matukar tarihi” wadda gungun shugabannin duniya suka sanya wa hannu, na nuna cewa “addu’ar miliyoyin al’umma ta karbu”.
Daga nan sai ya ce shugabannin sun samu nasarar tabbatar da “zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya”, sannan ya taya kowa murna.
Haka nan Trump ya gode wa shugaban Masar Abdul Fattah al Sisi bisa karrama shi da lambar girmamawa ta kasar ta ‘Order of the Nile’.