An sauya wa dakin Ka’abah sabuwar riga wato Kiswah, da aka kashe dala miliyan 6.5 wajen dinkata a safiyar wannan Asabar din.
An soma aikin sauya rigar tun daren ranar Juma’a bayan Sallar Isha zuwa asubahin Asabar, wanda ya zo daidai da ranar 1 ga watan Muharram na shekarar 1444 bayan hijirah.
- Dalibi Ya Daba Wa Wasu Dalibai 2 Wuka A Kan Musun Kwallon Kafa A Bauchi
- ‘Yan Daba Sun Yi Awon Gaba Da Injinan Yin Rijistar Katin Zabe A Jihar Legas
An kiyasata cewa nauyin sabuwar rigar ya kai kilogram 850, kuma a yanzu ya kasance irin wannan riga mafi tsada a duniya.
Wannan shi ne karon farko da aka sauya Kiswah wato kamar yada ake kiran rigar, a ranar 1 ga watan Muharram.
Kafin wannan lokaci ana sauya wa Ka’abah rigar ne a lokacin aikin Hajji, musamman a safiyar 9 ga watan Dhul Hijjah idan alhazai sun tafi hawan Arfah.
Karkashin jagorancin Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais da ke kula da manyan masallatai biyu mafiya daraja a duniya, ya ce an sauya lokacin sauya rigar Ka’abah ne bisa sabbin dokoki da shawarwari masarautar Saudiyya.
Mutane sama da 200 ne daga kafofin yada labarai ke cewa suka yi aiki akan rigar Ka’abah daga wajen dinkata har zuwa ta sanyata a jikin Kaaba.