Majalisar Dinkin Duniya ta ce 2023 ta kasance shekarar da aka sha fama da tashin hankali da rashin zaman lafiya a ƙasashen duniya.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya bayyana hakan a wani sako na bidiyo da aka fitar a jajibirin shekarar 2024.
- Adadin Wayoyin Salula Da Kamfanonin Kirar Su Suka Fitar A Kasar Sin Ya Karu Da 34.3% A Watan Nuwamba
- Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Gaskiya Ta Bayyana Kan Bullar Mata Masu Shan Jini
A cewarsa “bil’adama na cikin hali mawuyaci. Duniyarmu tana cikin babbar matsala. Shekarar 2023 ita ce shekarar da aka fi shiga hali mawuyaci a tarihi. mutane na mutuwa ta hanyar karuwar talauci da yunwa. Yaƙe-yaƙe da tashin hankali suna ƙaruwa da yawa Kuma amana ta yi karanci.
“Amma nuna wa juna yatsa da zuwa yaƙe-yaƙe ba za su kawo mafita ba”.
Gutteres ya yi kira da a hada kai cikin gaggawa da kuma hada karfi domin shawo kan kalubalen da ke gabansu. “Dole ne 2024 ta zama shekarar gina amana da maido da zaman lafiya.
“Dole ne mu hada gwiwa domin kawo mafitar wannan rigimar.
“Tare, zamu tashi tsaye wajen yakar wariya da kiyayya da ke haifar da guba game da dangantakar dake tsakanin kasashe da al’ummomi.
“Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da hada kan duniya don samar da zaman lafiya, ci gaba mai dorewa da kare hakkin dan Adam.
“Mu tabbatar da cewa shekarar 2024 ta zama shekarar gina amana kuma muna fatan zaman lafiya.”
A halin yanzu, Guterres ya bayyana damuwarsa kan karuwar talauci da yunwa. inda ya ce, wadannan kalubalen na ci gaba da zama barazana ga rayuwar jama’a a duniya.