Daga misalin karfe 6 na yammacin jiya Lahadi, an kawo karshen gargadi game da aukuwar girgizar kasa a mataki na farko a lardin Sichuan, inda kuma aka shiga matakin tsugunar da wadanda girgizar kasar ta shafa, da ma farfado da sassan da bala’in ya galabaita.
A ranar 5 ga wata, girgizar kasa ta auku a gundumar Luding ta lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, kuma ya zuwa misalin karfe 5 na yammacin ranar 11 ga wata, girgizar kasar ta hallaka mutane 93, a yayin da wasu 25 suka bace.
Yanzu haka, sassa daban daban a lardin na Sichuan na ci gaba da jinyar wadanda suka ji raunuka, inda ake iya kokarin ganin an sassauta nakassar sassan jiki da bala’in ka iya haifar musu.
A sa’i daya kuma, ana ci gaba da neman wadanda suka bace, baya ga kuma tsugunar da al’ummar da bala’in ya shafa a gidajen wucin gadi, tare da samar musu kayayyakin rayuwa.
Ban da haka, ana kokarin gyara hanyoyi da tsarin samar da wuta da ruwa, da sauran ababen more rayuwa da bala’in ya lalata, sai kuma sa ido, da ma yin hasashe ta fannonin girgizar kasa da yanayi da ruwa, don magance aukuwar karin wani bala’in da zai iya haifar da mutuwar mutane, ko jin raunukansu. (Lubabatu)