An shigar da manufar nan ta “Samar da al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama” cikin kudurori 3 da kwamitin farko na babban zaman MDD ya amince da su, a ranakun Talata da Alhamis.
Karo 6 ke nan a jere, ana shigar da wannan manufa cikin kudurorin kwamitin farko na zaman majalissar.
Kudurorin ukun da aka amince da su sun hada da na “Kara aiwatar da matakan zahiri na kandagarkin gasar jibge makamai a samaniya” da “Hana fara jibge makamai a samaniya ” da na “Samar da ci gaba a fannin fasahohin sadarwa daidai da bukatar tsaron kasa da kasa “. (Saminu Alhassan)