A shirye-shiryen sake rantsar da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan Jihar Gombe karo na biyu, tawagogin raye-raye da bushe-bushen al’adu daban-daban suka hallara a gdain Gwamnatin jihar domin nuna bajintarsu kan al’adu.
Kungiyoyin al’adun daban-daban sanye da kaya kala-kala sun baje kolin basirarsu, dake nuna bambance-bambancen al’adu da zaman lafiya a Jihar Gombe, tare da nuna goyon bayansu ga Gwamna Inuwa Yahaya da al’ummar Jihar Gombe kan bikin rantsarwar dake tafe a ranar Litinin.
Wasu daga cikin kungiyoyin al’adun da suka cashe a dandalin, sun hada da Laku daga Kaltungo, da Babu Nare daga Kwami, da Ngorda daga Yamaltu/Deba, da masu rawan al’adu na Waja daga Balanga, da Bitbit daga Billiri, da Fulani daga tawagar raya al’adu ta Jihar Gombe, da Dankwairon Gwamna da kuma masu kiɗdan al’adu na Yarbawa.
Sauran mawakan zamani na gida da suka nishadantar a taron sun hada da Sale El-square, da S-Niggar Gombe, da Kubura Sarkin Fulani, da Abbati Gombe da dai sauransu.
A takaitaccen jawabin da ya gabatar, Gwamna Inuwa ya gode wa wadanda suka shirya taron, da wadanda suka nishaɗdantar da kuma wadanda suka halarci gagarumin bikin.
Game da nasararsa ta kwanan nan na zama Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa ya bayyana nasarar a matsayin wata dama ta kara hidimtawa jama’a, inda ya sadaukar da matsayin ga dokacin al’ummar Jihar Gombe.
Ya ce, “Wannan matsayi ba nawa ni kadai ba ne, na dokacin al’ummar Jihar Gombe ne,” yana mai ba da tabbacin cewa ba zai ci amanar al’ummar jihar dama na Arewa ba.
Gwamnan ya yi amfani da damar wajen sabunta kira ga ‘yan siyasa musamman wadanda suka sha kaye a zabe, da su ajiye muradun su a gefe, su bada gudummawa don gina kasa.
Tun farko a jawabinsa na maraba, Farfesa Ibrahim Abubakar Ndodi wanda shi ne shugaban kwamitin tsare-tsaren sake rantsar da gwamnan, ya ce wannan dare na shagulgulan al’adu yana daga cikin shirye-shiryen rantsarwar wanda za a karkare gobe Litinin 29 ga wannan watan na Mayu, inda za a rantsar da Gwamna Inuwa Yahaya a karo na biyu.