Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC), Malam Nuhu Ribadu, ya janye karar da ya ke yi da ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani.
Ribadu, wanda ya rasa tikitin takarar gwamna a hannun Binani, ya kalubalanci nasarar da ta samu a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Adamwa, inda ya ce an tafka magudi a zaben fidda gwani da aka gudanar a watan Mayu.
Kotun ta soke zaben fidda gwanin da aka gudanar na ‘yan takarar gwamnan jam’iyyar gaba daya inda ta umurci Binani da cewa itama ba sai ta fito takarar ba a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar a zaben gwamna na 2023.
Sai dai makonni biyu da suka gabata wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Yola ta tabbatar da Binani a matsayin zababbiyar ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a Adamawa.
A wata wasika da ya aike wa jam’iyyar reshen jihar Adamawa, Ribadu ya bayyana matakin da ya dauka na kin zuwa kotun koli duk da cewa ya ki amincewa da hukuncin kotun daukaka kara da ta mayar da Binani.
Don haka ya bayyana kudurinsa na yin aiki domin ganin jam’iyyar ta samu nasara, inda ya yi kira ga dimbin magoya bayansa da su yi wa dukkan ‘yan takarar jam’iyyar aiki a zaben 2023.