‘Yan kasuwa sun yi asarar kadarori na miliyoyin Naira a wata gobara da ta tashi a wata kasuwa da ake sayar da wayar salula wacce aka fi sani da ‘GSM Village ‘ da ke kusa da kasuwar Kpata a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, gobarar ta afku ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, sakamakon wutar lantarki mai karfi inda masu shaguna basu iya fitar da komai ba daga shagunan sakamakon karfin gobarar.
- Jihar Kano Ce Za Ta Fara Aiwatar Da Sabon Mafi Karancin Albashi – Gwamna Yusuf
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 49 A Yankuna 226 A Kano — SEMA
Daya daga cikin ‘yan kasuwar da ibtila’in ya rutsa da su, Muhammed Yahaya ya bayyana cewa, “Wani ya kira ni da misalin karfe 5:30 na safe a yau cewa, kasuwa ta kama da wuta. Da isa wurin, shaguna da dama sun kone. Don haka, muka yi kokarin sanin ainihin musabbabin barkewar gobarar.
“Daga dukkan alamu ya zuwa yanzu, mutane sun shaida mana cewa, wutar lantarki ce ta yi karfi a lokacin da aka dawo da wutar a kasuwa.
“Mazauna gidajen da ke makwabtaka da kasuwar, sun ce, wutar ta lalata musu fankoki, fitilu da sauran abubuwan da ke amfani da wutar. A gaskiya, wannan na iya zama sanadin barkewar gobarar a kasuwar. Kadarorin miliyoyin naira sun lalace”.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kogi da ta shiga tsakani ta hanyar tallafa wa wadanda suka yi asarar kayansu da kudi da kuma sake gina kasuwar.