An gudanar da taron dandalin tattaunawa na masanan Sin da Afirka karo na 14 a birnin Kunming dake lardin Yunnan na kasar Sin a yau Talata, 20 ga wata, inda wakilai kimanin 100 daga Sin da kasashen Afirka fiye da 50 suka halarci taron tare da tattauna fasahohin mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa na kasar Sin da kasashen Afirka da kuma zamanintarwa irin ta kasar Sin.
Da yake tsokaci, Elia Kaiyamo, jakadan Namibia dake kasar Sin ya bayyana cewa, aikin zamanintar da kasa na da sarkakiya, domin kowace kasa tana da bambancin tarihi da al’adu da zamantakewar al’umma da tattalin arziki, don haka ya kamata a bi hanyoyi daban daban na zamanintarwa da suka dace da yanayin kasa, duk da cewa dukkansu suna da buri daya wato kyautata zaman rayuwar jama’a, da kawar da talauci, da raya zamantakewar al’umma mai inganci. Ya kara da cewa, fasahohin Sin na samun ci gaba sun shaida cewa, zamanintar da kasa tana da nasaba da bunkasuwar tattalin arziki, da sa kaimi ga samun daidaito a zamantakewar al’umma, da yi wa tsare-tsare kwaskwarima, da tafiyar da harkokin kasa yadda ya kamata.
A nasa bangare, shugaban kwalejin nazarin Afirka na kasar Sin Ye Hailin ya bayyana cewa, a matsayinsu na kasashe masu tasowa, Sin da kasashen Afirka suna kokarin zamanintar da kansu don samar da gudummawa wajen zamanintar da kasashe masu tasowa a duniya, da kuma kyautata harkokin jama’ar duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp