Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci a ajiye wani mutum mai suna Idris Kurma a gidan yari bisa zargin kashe matarsa, Aisha Idris, saboda ta ƙi yi masa ƙuli-ƙuli.
Mai shari’a Musa Dahiru ne, ya bayar da wannan umarnin bayan gurfanar da Idris a gaban kotu kan tuhumar kisan kai, wanda ya saɓa da sashe na 221 na dokar Penal Code.
- Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
- Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Goda da ke ka5ramar hukumar Shanono a Jihar Kano.
Lokacin da aka karanta masa tuhumar, Idris ya ce ba shi da laifi.
Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya nemi ƙarin lokaci domin gabatar da shaidunsa.
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.














