An tsinci gawar wani babban dan kasuwa Chukwunonso John Chukwujekwu mai shekaru 37 a wani dakin otel a jihar Bauchi.
Chukwujekwu, kafin mutuwarsa wanda ya fito daga karamar hukumar Anambra ta gabas yana da zama ne a kauyen Boi da ke karamar hukumar Bogoro, inda yake gudanar da kasuwancin sa.
Rahotanni sun ce, an tsinci gawarsa ce a otel din a ranar 1 ga watan Disambar 2022 bayan kwana biyu da sanar da bacewarsa, inda kuma har yanzu, ba a san musabbabin mutuwarsa ba.
Wani mamba a kungiyar alumma da ke taimaka wa ‘yansanda (PCRC) a yankin, Joel Danie ya tabbatar da mutuwar, inda ya ce, an kawo musu rahoton bacewarsa bayan an kai a ofishin yansandan na Bogoro.
Chukwujekwu an ce, da shi aka gudanar da shagalin bikin Igbo na karshen shekara a daren ranar larabar da ta gabata kasancewarsa yana daya daga cikin jigo a na alummar igbo da ke a yankin.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar SP Ahmed Wakili, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce, kwamishinan rundunar ya kuma bayar da umarnin a gudanar da bincike akan gawar.
Marigayi Chukwujekwu ya mutu ya bar mata daya Grace Chukwunonso da ‘ya’yansu biyu.