Rundunar ‘yansanda Jihar Bauchi, ta cafke wata mata mai suna Maryam Ibrahim ‘yar shekara 20 bisa zargin kashe uwargidanta, Hafsat Ibrahim da tabarya.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammad Wakil, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a yammacin ranar Litinin, ya ce an kama wanda ake zargin Maryam Ibrahim da ke kauyen Gar, Pali a karamar hukumar Alkaleri a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022.
- Jigon PDP Haladu Mohammed Ya Sauya Sheka Zuwa APC A Yobe
- Matasan Sin Masu Fasaha Sun Lashe Lambobin Yabo Bakwai A Gasar Duniya
A cewar kakakin, mijin matar mai shekaru 40 mai suna Ibrahim Sambo da ke kauyen Gar da ke karamar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi a ranar 22 ga Nuwamba, 2022, ya kai rahoton faruwar lamarin a hedikwatar ‘yansanda ta Maina-maji.
SP Wakil ya ci gaba da cewa, Ibrahim Sambo ya ruwaito cewa “a wannan rana da misalin karfe 12:00 na dare, matarsa ta biyu Maryam Ibrahim mai shekaru 20 da haihuwa a adireshin ta yi amfani da wata tabarya ta buga wa matarsa ta farko Hafsat Ibrahim a kanta.
Leadership Hausa ta tattaro cewa mijin marigayiyar ya sanar da ‘yansanda cewa a sakamakon haka, wadda aka kashe ta samu munanan raunuka kuma an kai ta cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke kauyen Gar inda wani likita ya tabbatar da mutuwarta.
“Lokacin da aka samu rahoton, wata tawagar jami’an tsaro da ke aiki a rundunar ta dauki matakin kama wadda ake zargin”, in ji kakakin.
Ya kara da cewa a lokacin da ake mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amince da aikata laifin da ake zarginta da shi.