Gwamnatin jihar Kano ta umurci kananan hukumomi 44 da ke jihar da su bayar da gudunmuwar kimanin naira miliyan 15.2 kowacce – jimillar naira miliyan 670 domin siya da gyaran ababen hawa ga majalisar masarautar Kano karkashin jagorancin Sarki Muhammadu Sanusi.
Kamar yadda wata wasika mai dauke da kwanan wata, 25 ga watan Maris 2025, da ke yawo a kafafen sada zumunta ke nunawa, za a cire kudaden ne daga asusun hadin gwiwa na kananan hukumomi sannan a biya wani kamfani mai zaman kansa, Sottom Synergy Resources Ltd. Ana sa ran kamfanin zai samar da sabbin motoci guda hudu tare da gyara wasu tsoffin motoci guda biyu.
- Artabu Tsakanin ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Banga Ya Ci Rayuka Da Dama A Bauchi
- An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A Nasarawa
Wasikar na dauke da sa hannun Daraktan sa ido na kananan hukumomi, Abubakar S. Dabo a madadin Kwamishinan Ma’aikatar kananan Hukumomin Jihar.
A wani bangare na wasikar na cewa, “An umurce ni da in isar da amincewar Gwamnati na fitar da jimillar kudi Naira miliyan 15,227,272.72 a asusun kowace karamar hukuma domin gyaran motoci biyu tare da siyo karin wasu guda hudu ga Majalisar masarautar Kano wanda kamfanin Sottom Synergy Resources Ltd zai dauki nauyin siyowa.
Wasikar ta kuma umurci shugabannin kananan hukumomin da su tabbatar an bi tsarin da ya dace wajen aiwatar da wannan umarni.
Duk da cewa, wannan umarnin ya janyo cece-ku-ce amma har zuwa rubuta wannan rahoto, gwamnatin jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da cece-ku-cen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp