Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni ga dukkan manyan makarantu a ƙasar nan da su miƙa cikakken rahoton kuɗaɗen Tertiary Education Trust Fund (TETFund) da ba a yi amfani da su ba cikin kwanaki 30, tare da gargaɗin cewa kuɗaɗen da suka rage ba tare da dalili ba za a karɓe su a sake karkatar da su zuwa muhimman aiyuka.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarni a taron da ya gudanar da shugabannin jami’o’i, da kwalejojin fasaha, da kwalejojin ilimi a Abuja. Ya bayyana damuwarsa cewa miliyoyin kuɗaɗen da aka ware don gina makarantu da bunƙasa ilimi suna killace ba tare da an yi amfani da su ba saboda matsalolin gudanarwa da jinkiri wajen aiwatar da ayyuka.
- Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
- TETFund Ta Dakatar Da Tura Malamai Karatu Ƙasar Waje
Alausa ya ce dole ne dukkan makarantu su gabatar da rahoton kuɗaɗen da ba su kashe ba domin tantancewa, yana mai jaddada cewa “ba za a ƙara amincewa da ajiye kuɗaɗen TETFund ba tare da hujja mai ƙarfi ba.” Ya kuma ce duk shirin sayen kaya ko aiki ya zama cikin tsarin da aka amince da shi don kaucewa jinkiri.
Ministan ya bayyana cewa za a ƙaddamar da shirye-shiryen horaswa don inganta gudanar da ayyuka, da bin doka da rahotanni, tare da yin nazarin duk bayan wata uku domin tabbatar da bin ƙa’ida. Ya ce za a kafa dandalin wallafa bayanai na gaskiya (public dashboard) domin jama’a su riƙa ganin yadda ake raba da kuma kashe kuɗaɗen TETFund.
Ya ƙara da cewa wajibi ne shugabannin makarantu su nuna gaskiya da riƙon amana wajen amfani da kuɗin jama’a. “TETFund ya zama dole ya tabbatar da bin ƙa’ida da gaskiya, kuma dole shugabannin cibiyoyi su ɗauki alhakin tabbatar da aiwatar da ayyuka cikin lokaci,” in ji shi.
Tun a baya TETFund ta yi gargaɗin cewa za ta cire kuɗaɗen da ba a yi amfani da su ba daga hannun makarantun da suka gaza wajen aiwatar da ayyuka. A shekarar 2025, hukumar ta raba ₦1.6 tiriliyan ga manyan makarantu a faɗin ƙasar, inda aka fi mai da hankali kan tsaro, da inganta cibiyoyi, da kula da lafiya.