An wallafa wani littafi mai kunshe da tambaya da amsa a kan Tunanin Xi Jinping game da wayewar kai a bangaren kiyaye lafiyar muhalli.
Littafin wanda ya bayyana tunanin Xi kan batun, ta hanyar tambaya da amsa, ya yi bayani dalla-dalla kan muhimmanci, tsarin kimiyya, jigo, tasiri, da abubuwan da ake bukata a aikace daga Tunanin Xi Jinping a kan wayewar kai game da kiyaye lafiyar muhalli. (Abdulrazaq Yahuza Jere)