A ranar 17 ga watan Afrilun nan, yayin ziyarar aiki ta shugaba Xi jinping a kasar Cambodia, an yi bikin kaddamar da shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Cambodia, wanda CMG ya shirya a birnin Phnom Penh.
Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Inda ya ce a shirye CMG yake ya yi aiki tare da abokai daga sassan daban daban na kasar Cambodia domin ci gaba da zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da samar da karin haske a fannin musayar al’adu, da sanya sabon kuzari a aikin gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tsakanin Sin da Cambodia. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp