Albarkacin cika shekaru 55 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Italiya, an shirya bikin kaddamar da shirin talibijin mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ya gabatar, a jiya Laraba a birnin Rome, hedkwatar kasar Italiya. Za a fara watsa wannan shiri a kafofin yada labarai na kasar fiye da 30.
An dauki da kuma tsara wannan shiri ne a garin Zhengding na lardin Hebei da Xiamen na lardin Fujian da Hangzhou na lardin Zhejiang da kuma Dunhuang na lardin Gansu da sauran wuraren da Xi Jinping ya taba kai rangadi ko aiki a can, don yin karin haske kan kokarin da Sin take yi wajen zakulo mafarin al’adun Sinawa, da kiyaye kayayyakin al’adu da sauran al’amura, matakin da ya bayyana dogon tarihin al’adun Sinawa dake ma’ana mai zurfi, da kayatattun al’adu masu burgewa. (Amina Xu)














