An gudanar da taron gangamin wayar da kan al’ummar da ke a garin Rigachikun a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, musamman iyaye kan alfanun tura ‘ya’yansu mata makarantar sakandare, domin su ci gajiyar shirin bunkasa ilimin ‘ya’ya mata na AGILE.
A hirarta da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Ko’idinatar shirin na Jihar Kaduna, Maryam Sani dangaji ta ce, makasudin taron shi ne, domin wayar wa iyayen da ke a garin Rigachikun da kewaye kai kan mahimmancin su tura ‘ya’yansu mata zuwa makarantar sakandare da kuma tallafin kudin karatu, da Bankin Duniya ke turawa kai tsaye zuwa ga asusun bankin na daliban mata.
- Aikin Bututun Gas Na Nijeriya – Morocco Na Ƙara Samun Ci Gaba
- Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Ƙarshe Tsakanin Chelsea Da PSG
Maryam ta ce, shirin ya faro ne daga matakin makarantar firamare zuwa na sakandare, musamman domin su ci gajiyar shirin.
Ta ce, wannan wayar da kan shi ne karo na uku, inda ta ce, muhimmancin wayar da kan shi ne, yawanci wasu iyayen ba su da masaniya kan shirin, wanda kuma shi ne, Bankin Duniya ya ga ya kamata a zo yankin domin a kara wayar da kan iyaye kan alfanun Shirin.
Maryam ta yi nuni da cewa, tallace-tallace, musamman a tsakanin ‘ya’ya mata bai da wani alfanu, amma samun ilimin zamani na da babban tasiri ga rayuwar mata da kuma al’umma.
Ko’odinitar ta ce a baya a karkashin shirin, ana bayar da tallafin naira 5,000, wanda ya koma koma naira 15,000, kuma a yanzu ya koma naira 25,000.
Mayarma ta kara da cewa irin wannan tallafin zai taimaka wa iyayen daliban mata wajen saya musu abubuwa irinsu takalmin zuwa makaranta, ko takardun karatu ko Biro da sauran kayan karatu.
Ita ma daya daga cikin ma’aikatan Bankin Duniya, Dakta Basir Rufa’I ta ce, an wayar da kan ‘ya’ya matan kan yadda za su rajista a karkashin shirin.
Ta ce, akwai kuma ka’ida da aka gindiya ga wadanda su ci gajiyar shirin, wanda ta ce, shi ne na zuwa makaranta da suka samu maki kaso saba’in a cikin dari a cikin rajistarsu ta zuwa makaranta, wanda ta haka ne za su iya samun cin gajiyar tallafin.
Wasu daga cikin iyayen da ‘ya’yansu mata suka ci gajiyar shirin, Fatima Abubakar da Alh. Idris Maiwada, sun yaba da shirin tare da gode wa gwamnatin Kaduna kan goyon bayan da take ci gaba da bai wa shirin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp