Manya da kananan ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen waje, sun shirya liyafa a baya bayan nan, domin murnar cikar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin shekaru 74 da kafuwa.
Shugabannin hukumomin duniya da na kasashe da mutane daga dukkan fannonin rayuwa, sun halarci liyafar ko gabatar da jawabai ta hanyoyi mabanbanta domin taya kasar Sin murna da kuma yabawa ci gaban tattalin arziki da zaman takewa da ta samu, suna masu alwashin zurfafa hadin gwiwa da ita a bangarori daban-daban domin bayar da kyakkyawar gudunmuwa ga zaman lafiya da ci gaban duniya.
- Kasar Sin Ta Zama Abar Koyi Ga Goyon-Bayan Hadin-Gwiwar Kasashe Masu Tasowa
- Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba
A nata jawabi, darakta janar ta hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce kasar Sin ta samu dimbin ci gaba kuma ta amfanawa kasashe masu tasowa da kyawawan sakamako.
Shi kuwa sakataren gwamnatin kasar Kenya, Musalia Mudavadi, ya bayyana yayin liyafar da ofishin jakandacin Sin a Kenya ya shirya cewa, kwarin gwiwar kasar Sin na gwagarwamayya cikin jarumta domin ci gaban kasar, ya cancanci yabo.
A nasa bangaren, ministan kula da harkokin cinikayya da masana’antu na Zambia Chipoka Mulenga, jinjinawa dangantakar dake tsakanin kasarsa da Sin ya yi, yana mai cewa ana tafiyar da dangantakar bisa ka’idoji na daidaito da mutunta juna da burin samun ci gaba na bai daya. (Fa’iza Mustapha)