Bikin yaye ɗaliban kwalejin ilimi ta tarayya da ke Yola FCE wanda da shi ne karo 15, ɗaya ne daga cikin ɓangarori uku na taron da suka haɗa bikin cikar Kwalejin shekaru 50 da aka ƙaddamar a lokacin gudanar da taron.
Da ya ke jawabi a taron shugaban kwalejin, Mohammad Usman Degereji, ya bayyana cewa tun da aka kafa ta, makarantar ta samu ci gaba a dukkan fannonin da suka shafi kwalejin.
- Batun ‘Yan Mata Masu Yanga Wajen Tsallaka Titi
- Mun Shirya Ƙirkiro Sabbin Masarautu A Adamawa – Fintiri
Shugaban ya lissafo wasu daga cikin manyan nasarorin da kwalejin ta samu da suka haɗar da kafa cibiyar ɗalibai don sauƙin samun bayanan sakamako, da bayar da shaidar karatun ilimi a fannonin ilimi daban-daban.
Wasu daga manyan nasarorin da ta samu sun haɗa da samar da motocin bas bas dake ɗaukar ma’aikata da dalibai kyauta na tsawon watanni uku, sakamakon cire tallafin man fetur, da rarraba kayan abinci ga ɗalibai domin sauƙaƙa wahalhalun da ake ciki sakamakon cire tallafin, da gyaran asibitin kwalejin da kuma samar masa kayan aiki, da magunguna hadi da kwararren likita daga FMC Yola.
Shugaban ya kuma godewa gwamnatin tarayya, da gwamnatin jihar Adamawa da kuma hukumar TETFUND, da ma’aikatan Kwalejin da kuma ɗalibai bisa goyon baya da fahimtar da suka bayar na cimma nasarorin da kwalejin ta samu.
A nasa jawabin, ministan Ilimi Tunji Alausa, wanda ya sami wakilcin Dakta Yusuf Sa’eed, ya taya shugaban Kwalejin da hukumar gudanarwa murnar samun ci gaba ya kuma yi alƙawarin gabatar da buƙatar Kwalejin na ingantawa a gaban ministan ilimin.