Albarkacin halartar kwarya-kwaryar taro na 31 na shugabannin kungiyar APEC, da gudanar da ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke yi a kasar Peru, a jiya Jumma’a an yi bikin kaddamar da zababbun kalaman shugaba Xi Jinping “Zango na 3” da harshen Sifaniya.
Kafar CMG ce ta kaddamar da shirin a birnin Lima, fadar mulkin kasar ta Peru, kuma shugabar kasar Dina Boluarte ta taya murnar watsa shirin a Peru ta wani sakon bidiyonta da aka watsa. Mutane kimanin 200 daga sassan rayuwa daban daban sun halarci bikin kaddamar da shirin, ciki har da ’yan siyasa, da masana tattalin arziki, da na fannin raya al’adu, da ’yan jarida, da malaman jami’o’i da sauran su.
Da take tsokaci game da hakan, shugaba Boluarte, ta ce kaddamar da shirin a Peru, ya sake karfafa tushen kawancen kasar da Sin. Baya ga gina gadar sada zumunta tsakanin musamman matasan Peru da na Sin, da kara fahimtar da jama’ar kasarta tarihi, da yanayin falsafar kasar Sin mai dogon tarihi, a daya bangaren ya sake jaddada kwazon shugaba Xi Jinping a fannin gado, da wanzar da wayewar kan kasar Sin ta shekaru 5000, da shigar da ita cikin manufar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan)