A jiya Litinin da dare ne, sashen fadakar da jama’a na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), da ma’aikatar harkokin al’adu da yawon shakatawa ta Sin, da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG suka kira bikin kade-kade a dakin nune-nunen tarihin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, domin taya murnar cika shekaru 104 da kafuwar Jam’iyyar.
A yayin bikin, an yi kade-kade guda 17, ciki har da kidan Symphony, da na salon rera waka tare, da kuma ta hanyar amfani da kayan kida na gargajiya da dai sauransu.
Wakilan da suka hada da masu lashe lambar yabo ta “The July 1st”, da mutanen dake da nagartattun halaye, da jami’an JKS, da dai sauran wakilai daga bangarori daban daban fiye da 800 ne suka halarci bikin.
Haka kuma, za a watsa wannan bikin kade-kade ta wasu tashoshin talabijin na CMG a yau Talata 1 ga watan Yuli da dare. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp